Ana xaukar gaskiya a matsayin mabuxin tsira da rabauta a duniya da lahira, hakan kuma yana bayyana a vangarori uku manya:
1- Gaskiya tare Allah: Wannan tana samuwa ta hanyar yin ikhlasi a imani da aiki na gari da xabi’un sam-barka. Hakanan ta haxa da gaskiya a yaqini da niyya da tsoron Allah. Ana iya yin gane wannan gaskiyar ta hanyar lizimtar ayyukan xa’a da nisantar laifuffuka, da yin kwalliya da siffofin muminai masu gaskiya kamar yadda ya zo a cikin Alqur’ani.
2- Gaskiya a karan-kan mutum: Ana so mutum ya zamo mai faxa wa kansa gaskiya, mai yi wa kansa hisabi, mai gyara aibukan da yake tattare dasu. Hakanan wajibi ne mutum ya nisanci faxawa tarkon burace-burace na qarya da soye-soyen zuciya, ya kuma zamo mai faxakuwa game da haxarin zuciya da makircinta, ya yi aiki tuquru don tsarkaketa da miqar da ita ta yi daidai da koyarwar addini.
Ya kamata mu zamo masu faxa wa kanmu gaskiya, mu kalli aibukanmu mu tsayu mu gyara su. Yi wa kai hisabi hanya ce da muminai suke bi, kuma alama ce ta masu kaxaita Allah da bauta, kuma adireshi ne na masu tsoron Allah. Shi mumimi mutum ne mai kiyaye dokokin Ubangijinsa, mai kuma yi wa kansa hisabi ne, mai kuma neman gafarar zunubansa ne, yana sane da cewa, haxarin zuciya abu ne mai girma, kuma cutarta aba ce mai cutarwa, makircinta kuma babba ne, sharrinta kuma mai yaxuwa ne. Lalle ita rai mai yawan umarni da mummunan aiki ce, kuma mai yawan karkata ce zuwa ga son zuciya, kuma mai kira ce zuwa jahilci, kuma mai yin jagora ce zuwa ga halaka, mai kuma karkata zuwa ga wargi ce, sai fa ga wanda Allah ya yi wa rahama. Don haka kada a qyaleta da abin da take so, domin ita mai kira ce zuwa ga xagawa. Duk wanda ya yi mata biyayya, to za ta ja shi zuwa ga munanan ayyuka, ta kuma kira shi zuwa ga abubuwan qi, ta kuma kutsa da shi cikin abubuwan da ba a so, musibunta ababen mamaki ne, abubuwan da suke fizgarta ababen tsoro ne, sharrikanta masu yawa ne, duk wanda ya bar ragamar ransa ta yi xagawa, to wutar jahimu ita ce makomarsa a ranar alqiyama. (To (a wannan ranar) duk wanda ya yi xagawa. Ya kuma fifita rayuwar duniya. To lalle (wutar) jahimu ita ce makomarsa). [Nazi’at: 37-39]. Akasinsa kuma shi ne (Duk wanda kuma ya ji tsoron tsayuwa gaban Ubangijinsa, ya kuma hana zuciya bin abin da take so. To lalle Aljanna ita ce makoma.) [Nazi’at: 40-41]
3- Gaskiya ga mutane: Wannan ya qunshi gaskiya a maganganu da ayyuka da halaye. Ana xaukar mu’amalantar mutane da gaskiya a matsayin dalili a kan gaskiyar imanin mutum, ita kuma qarya a matsayin dalili a kan munafuncin mutum. Wajibi ne Musulmi ya kasance mai nasiha ga ‘yan’uwansa Musulmi, mai kiyaye amana da yarjejeniya, ya kuma yi qawa da kyawawan xabi’u a yayin mu’amalarsa da wasu.
Dole ne gaskiya ta zama siffa mai lizimtar Musulmi a dukkan vangarorin rayuwarsa, kuma yin hakan yakan zama hanyar rabauta da tsira a duniya da lahira.
Katika masu alaka
Nuna katika