Amana Nauyi ce Mai Girma a Musulunci

Amana Nauyi ce Mai Girma a Musulunci

Amana Nauyi ce Mai Girma a Musulunci

79 32


Muhimmancin kyawawan halaye da tadoji masu girma wurin samar da nutsuwa da dacewa ga mutum da kuma al’umma. Kuma yana qarfafa cewa, wajibi ne a riqa aiwatar da waxannan xabi’un a kowane hali da kowane yanayi. Xabi’ar amana tana daga cikin mafi muhimmancin waxannan xabi’un. Kuma ita amana ba ta taqaita a kan kiyaye dukiya ba kawai, a’a ta haxa da kiyaye magana da aiki da mu’amalolin yau da gobe da ibadu da alqawurra da abubuwan da aka lizimta wa mutum da abin da ya shafi lafiya da kafafen isar da saqo da ke jikin mutum da wasunsu.

Amana wani vangare ne kuma jigo na halittar dan’adam da kuma addini. A bisa xabi’ar mutane sukan so su karkata zuwa ga amintaccen mutum su kuma aminta dashi. Nassoshi sun zo da suke kwaxaitar da Musulmi a kan koyon xabi’ar amana daga Musulunci da yin qawa da ita a dukkan vangarorin rayuwa, suna masu tabbatar da cewa, dukkan wanda zai yi qawa da riqon amana, to zai mai yarda da kansa kuma mutane da za su karve shi, kuma zai shiga cikin rahamar Allah da ihsaninsa.

An wayi gari amana ta yi qaranci saboda gafala game da abin da ya shafi lahira da son duniya da nisantar koyarwar addini. Don haka ake gargaxin dukkan al’ummar da aka rasa amana a cikinta da cewa, tana cikin al’umma mafi lalacewa. Hakanan kuma ana cewa, gushewar amana zai faru ne a sannu-a sannu tare da munanan ayyuka da ake yi, wanda hakan zai bayu ga canja abubawan da suke sune gaskiya, da yin qarya game da abubuwan da suka faru. Akwai nassin hadisin Annabi da ya zo yake nuni da gargaxi game da wani zamani da zai zo wanda za a riqa gaskata maqaryaci a riqa qaryata mai gaskiya, a aminta da maha’inci, amintacce kuma a mayar da shi maha’inci.

Tawaya a amana yana bayuwa zuwa ga tawaya a imani. Hadisin Annabi ya zo da siffar yadda za a cire amana daga zukata, amana ta zama wata aba ce ‘yar kaxan har ya zamana ana yabon wanda babu wani alheri ko imani a tattare dashi.

Katika masu alaka

Nuna katika

icon

Yi tarayya