Muhimmancin Gaskiya a Musulunci

Muhimmancin Gaskiya a Musulunci

Muhimmancin Gaskiya a Musulunci

85 37

Ana xaukar gaskiya a matsayin xaya daga cikin turakun da suke ba da gudunmawa wurin rabautar mutum da kuma samun dacewa. A kanta ne kai-komon alaqar mutane ta aminci take qulluwa, kuma ita ce tushen yarda tsakanin xaixaikun mutane. Gaskiya ita ce tufar cin nasara da kuma ruhinsa, yayin da qarya kuma ta zama babban tushen faxuwa da tavewa. Dukkanin al’ummu da addinai sun haxu a kan ganin darajar gaskiya da muhimmancinta yayin gina al’ummomi da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Dukkan addinai musamman Musulunci sun ba da babbar kulawa game da sha’anin gaskiya, sun kuma sanya ta daga cikin xabi’u da ake so, wanda ya wajaba ga duk wani mumini ya yi kwalliya da ita. A Musulunci, gaskiya tana cikin tushen addini, kuma tana cikin turakun addini. Tana xaya daga cikin siffofin da suke bambance tsakanin mumini na gaskiya da kuma munafuki. Manzon Allah Annabi Muhammadu, salatin Allah da amincinsa su tabbata a gare shi, ya tabbatar da cewa, lalle yin gaskiya yana bayuwa zuwa ga samun nutsuwa da hutun rai, a yayin da yin qarya yake bayuwa zuwa ga samun kokwanto da tababa.

Gaskiya ita ce ma’aunin sauran kyawawan xabi’u, kuma ita ce hanya mafi dacewa da za a bi don a isa zuwa ga maxaukakan matsayai. Duk wanda ya yi qawa da gaskiya, to za a iya azurta shi da hangen nesa na gaskiya da kuma hanya mai qarfin gaske. Gaskiya wata takobi ce da take sare kan varna, kuma hanya ce ta tsira daga wahalhalu da abubuwan tashin hankali.

Annabi salatin Allah da amincinsa su tabbata a gare shi ya bayyana cewa, lalle mumini zai iya zamowa matsoraci ko marowaci, amma ba zai yiwu ya zamo maqaryaci ba. Wannan yake nuni zuwa ga cewa, gaskiya wani vangare ne na imanin mumini wanda ba a iya rabata da shi. Gaskiya sababi ce ta rabauta da tsira a duniya da lahira, kuma tana daga cikin abubuwan da ake kimsa wa masu gaskiya a maganganunsu da ayyukansu.

Saboda kyawun gaskiya hankali ma yana kira zuwa gareta, kamar yadda yake qin kishiyarta. Addini ma ya yi umarni da a yi gaskiya ya kuma kwaxaitar da yinta. Annabi salatin Allah da amincinsa su tabbata a gare shi yana cewa: “Wasu mutane daga cikin waxanda suka gabaceku suna tsaka da tafiya, sai kwatsam ruwan sama ya sauko, sai suka shiga wani kogo suka fake, sai wani dutse ya gangaro ya rufe su. Sai sashinsu ya ce da sashi, lalle fa ku sani wallahi babu abin da zai tserar da ku in ba gaskiya ba, don haka kowane mutum daga cikinku ya yi addu’a da abin da ya san ya yi gaskiya yayin da ya aiwatar dashi”. Har zuwa qarshen hadisin. Sai ya zamana dalilin tsiransu shi ne gaskiyar da suka yi wa Allah. Mutuntuka aba ce da ke bayuwa zuwa aikata gaskiya kuma tana zaburarwa zuwa ga aikata gaskiya. Labarawa sun kasance ba sa son su ga an samu qarya daga wajensu, suna son su ga sun shahara da gaskiya. Hakanan kuma ana lissafa qarya daga cikin alamomin munafunci.

Katika masu alaka

Nuna katika

icon

Yi tarayya