Gaskiya: Ginshiqin Xabi’u Kuma Mabuxin Aljannatai

Gaskiya: Ginshiqin Xabi’u Kuma Mabuxin Aljannatai

Gaskiya: Ginshiqin Xabi’u Kuma Mabuxin Aljannatai

74 33

Gaskiya ita ce ginshiqin kyawawan xabi’u, kuma gaskiya tana cikin mafi muhimmancin siffofin Musulmi na gaskiya. Kuma gaskiya ta qunshi vangarori da dama, daga cikinsu akwai:

1-    Gaskiya a magana: Dole ne Musulmi ya zamo mai gaskiya a dukkan abin da zai faxa, saboda yin gaskiya dalili ne da yake nuna imani mutum, yin qarya kuma dalili ne da yake nuna munafuncin mutum.

2-    Gaskiya a ayyuka: Ya kamata ayyukan Musulmi su dace da maganganunsa, kuma ya zamana baxininsa ya yi daidai da zahirinsa.

3-    Gaskiya a niyya da nufi: Dole ne niyyar Musulmi ta zamo an tsantsantata ga Allah Ta’ala, ba tare da an gaurayata da wani abu na riya ko neman duniya ba.

4-    Gaskiya a qudiri: Ya wajaba a kan Musulmi ya kasance mai tabbatuwa a kan qudirinsa, kada ya canja shi ko ya musanya shi bayan ya yi wa Allah alqawari a kan wannan qudirin. Allah Ta’ala yana cewa a cikin mabuwayin littafinsa: (Daga cikinsu kuma akwai waxanda suka yi wa Allah alqawarin cewa: “Idan Ya arzuta mu daga falalarsa, to lalle tabbas za mu riqa ba da sadaka, kuma lalle tabbas za mu zama cikin mutane salihai.”. To lokacin da Ya arzuta su xin sai suka yi rowa da ita (sadakar) suka kuma ba da baya suna masu bijirewa. Sai Ya gadar musu da munafunci a cikin zukatansu har zuwa ranar da za su gamu da Shi, saboda sava wa alqawarin da suka yi wa Allah da kuma qaryatawar da suka zamanto suna yi).  [Tauba: 75-77]

5-    Gaskiya a matakan addini: Dole ne Musulmi ya kiyaye matsayin imaninsa, ya kums kasance mai gaskiya a dogaronsa da tsoronsa ga Allah.

6-    Gaskiya a tsoro: Ya kamata tsoron Allahn Musulmi ya zamo na gaskiya, kuma hakan ya bayyana ta fuskar nisantar laifuffuka da abubuwan da suka sava wa shari’a.

7-    Gaskiya a ayyukan zuciyoyi: Dole ne zuciyar Musulmi ta zamo mai fuskantar Allah da gaskiya da ikhlasi a yayin dukkan ibadu da dukkan yanayi.

Ta dalilin yin kwalliya da waxannan siffofi ne, Musulmi zai rayu irin rayuwar da take cike da nutsuwa da kwanciyar hankali, ya kuma zama abin buga misali ga mumini na gaskiya wanda aikinsa yake dacewa da maganarsa, ya kuma zamo a mafi darajojin imani da taqawa.

Katika masu alaka

Nuna katika

icon

Yi tarayya