Ka yi haquri don ka cimma manufarka

Ka yi haquri don ka cimma manufarka

Ka yi haquri don ka cimma manufarka

79 31


Dukkan wata manufa da take da muhimmanci ana buqatar haquri da dagewa don a cimmata, wannan ya haxa da abin da yake da alaqa da yin zarra a sha’anin karatu, ko gina wani babban aiki ake so ya yi nasara, ko abin da ya shafi bunqasa kai, to lalle ana xaukar haquri a matsayin abokin tafiya a irin wannan tafiyar yayin da muke fuskantar rashin cin nasara.

 

A tsarin tafiyar da rayuwa, haquri shi ne abokin da yake shiryar da mu zuwa ga cin nasara. Kowace manufa tana da buqatar a jajirce a kuma ba ta lokaci. In ba a yi haquri ba, to nan da nan za a juya da baya a kauce hanya. Haquri yana koyar da mu ya ya za mu fuskanci qalubale ba tare da mun rasa fatan mu na tabbatar da mafarkinmu ba. Lalle haquri yana tunatar da mu cewa, a haqiqanin lamari dukkan wani jinkiri mataki ne na havaka da bunqasa da kuma ci gaba.

 

Haquri yana haska kyawun ruhin xan’adamtakar mutum da kuma ikonsa a kan tsallake qalubale ta hanyar imani da kyakkyawan fata.

 

Haquri a haqiqaninsa yana nuna irin qarfin da ke taskace a cikin ran mutum, wanda yake ba shi dama na fuskantar qalubalen rayuwa ta hanyar tabbatuwa da samun nutsuwa. Domin yana nufin wanzuwar ruhin mutum yana rataye da irin mafarkinta da kuma fatanta, har a cikin lokuta  mafiya tsananin duhu da wahala.

 

Haquri shi ne kafaffen imani da cewa, lallai bayan kowane tsanani akwai sauqi, kuma kowane tsanani yana da mafita, kuma komai nisan dare gari zai waye

Katika masu alaka

Nuna katika

icon

Yi tarayya