Haquri da Afuwa Mabuxan cin Nasara

Haquri da Afuwa   Mabuxan cin Nasara

Haquri da Afuwa Mabuxan cin Nasara

86 29


Yin haquri bai taqaita a kan juriya yayin tsanani ba kawai, a’a ya haxa da yin ado da qawa da kyawawan xabi’u waxanda ake yaba yayin mu’amalantar sauran mutane.

 

Yin haquri a bisa cutarwa da yin afuwa yayin da ake da ikon ramawa, siffofi ne da Allah yake sonsu, yake kuma ba da kyakkyawan sakamako idan an yi su.

 

Haquri yana koyar da mu ya ya za mu yafe qullacin da ke cikin zuciya, don akwai hutun zuciya a cikin kawar da kai, kuma yana gina gadojin soyayya da ‘yan’uwantaka a tsakanin mutane.

 

Haquri yana bayyana a mafi kyawun siffarsa yayin da ya kasance ya haxu da aiki na gari. Mai haquri ba ya wadatuwa da zaman jira, yana yin aiki yana qoqari da kai-kawo a bayan qasa yana mai kuma dogaro da Allah, yana mai imani cewa qoqarinsa ba zai tafi a banza ba.

 

Haquri da aiki na gari ‘yan biyu ba sa rabuwa, kowane xaya daga cikinsu yana cika xayan, kuma suna haskaka hanya don cimma manufar da aka sa a gaba

Katika masu alaka

Nuna katika

icon

Yi tarayya