“Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daxi mai ruxarwa”.
Nuna katika
Yayin da ake cikin hayaniyar jama’a....to akwai wani sauti da yake can cikin ranka wanda babu mai iya jin sa in ba kai ba. Don haka Alqur’ani yana magana ne da wannan vangaren mai zurfi da yake cikin ran mutum. #Hasken_Alqur’ani #Gasar_cin_kofin_duniya #Alqur’an #Dan’adamtaka #Musulunci
Xan wasa yakan iya faxuwa a wata gasa...amma kuma ya dawo da qarfinsa. Hakanan shi ma mutum zai iya farowa daga farko. Alqur’ani ba ya rufe qofar kyakkyawan fata.
“Kuma Shi Yana tare da ku a duk inda kuka kasance”. [Hadid: 4]
Miliyoyin mutane suna kallon gasa-gasa a wurare mabambanta... sai dai mutum yana da buqatuwa zuwa ga wanda zai saurare shi ya fahimce shi da gaskiya.
“Lalle tsanani yana tare da sauqi” [Sharh: 6]
Yayin da ake cikin kaxaici ko damuwa...Alqur’ani yana magana game da kusancin Allah ga mutum. #Hasken_Alqur’ani#Imani#Saqon_Alqur’ani#Zuciyar_xan’adam#Qwallon_qafar_duniya.