“Kuma Shi Yana tare da ku a duk inda kuka kasance”. [Hadid: 4]
Nuna katika
Yayin da ake cikin hayaniyar jama’a....to akwai wani sauti da yake can cikin ranka wanda babu mai iya jin sa in ba kai ba. Don haka Alqur’ani yana magana ne da wannan vangaren mai zurfi da yake cikin ran mutum. #Hasken_Alqur’ani #Gasar_cin_kofin_duniya #Alqur’an #Dan’adamtaka #Musulunci
Bayan an gama hayaniyar...to mutum zai zamana shi kaxai daga shi sai zuciyarsa. To a nan ne tambayoyi na gaskiya suke farawa. #Hasken_Alqur’ani#Bayan_wasa#Gaskiya#Hasken_Alqur’ani#Nutsuwar_Zuciya
“Ku saurara, da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa”. Ra’ad: 28
“Sannan kuma ga Ubangijinku za a komar da ku”. [Sajda: 11]
“Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daxi mai ruxarwa”.
“Lalle Allah Yana tare da masu haquri”. [Baqara: 153]