“Ku saurara, da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa”. Ra’ad: 28
Nuna katika
“Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daxi mai ruxarwa”.
“Lalle tsanani yana tare da sauqi” [Sharh: 6]
Ko da ya kasance ana cikin mafi tsananin lokuta, to a tuna fa akwai wata qofar da za a samu haske ta wurinta. Kuma wannan shi ne abin da Alqur’ani yake tunatar da mu game da shi. #Hasken_Aqur’ani#Kyakkyawan_fata#Kofin_Duniya2026#Imani#Alqur’ani
Yayin da ake cikin kaxaici ko damuwa...Alqur’ani yana magana game da kusancin Allah ga mutum. #Hasken_Alqur’ani#Imani#Saqon_Alqur’ani#Zuciyar_xan’adam#Qwallon_qafar_duniya.
Bayan qarfin da muke iya gani a wasanni... to akwai wani kuma da yake wahala yake kuma jin tsoro yake yin rauni. Alqur’ani yana yin magana game da xan’adam ne da gaskiya da kuma rahama.
Yayin da ake cikin hayaniyar jama’a....to akwai wani sauti da yake can cikin ranka wanda babu mai iya jin sa in ba kai ba. Don haka Alqur’ani yana magana ne da wannan vangaren mai zurfi da yake cikin ran mutum. #Hasken_Alqur’ani #Gasar_cin_kofin_duniya #Alqur’an #Dan’adamtaka #Musulunci