Yan’uwantaka da kuma Kaxaituwa."
Muna rayuwa a wata irin duniya wadda take cike da hayaniya da samun savani. Sai dai kuma zukata suna yin kamanceceniya sama da yadda muke qudurcewa.
Kowane mutum yana xauke da wani labari mai raxaxi game da kansa. Hakanan yana xauke da labarin da ke nuna juriya da tsoro da kuma kyakkyawan fata game da rayuwarsa.
Don haka ka miqa wa xan’uwanka hannunka ko wani makusanci ko ka miqa hannunka zuwa ga wani mutum wanda ba ka sanshi ba, yana haifar da wani yanayi na musamman, wanda zai sa mutum ya ji cewa, ba fa shi kaxai ba ne, ya kuma san cewa duniya ba wuri ne mai sanyi ba a kowane lokaci.
Alqur’ani yana cewa: “Lalle muminai ‘yan’uwan juna ne, sai ku yi sulhu a tsakanin ‘yan’uwanku. Kuma ku kiyaye dokokin Allah don a ji qan ku.” [Hujurat: 10]
‘Yan’uwanta ba ta taqaita a kan alaqa ta addini ba, ‘yan’uwataka wata mahaxa ce ta xan’adamtaka mai zurfin gaske.
Kaxaituwa kuma ba shi ne ka yi tunani irin yadda kowa ya fahimci abu ba, a’a kaxaituwa shi ne, mu girmama savanin da ke tsakaninmu, mu gina hanyoyin rahama a tsakaninmu.
Ka yi tunani game da duniyar da savanin da ka samu da wani ba zai raba ka da kowa ba. Ta yadda kowace zuciya za ta riqa jin cewa wane na ta ne. Sannan kowane mutum zai iya bayar da kyauta. Sannan kowane hannu zai iya miqawa ba tare an dawo masa da sakamako ba.
To wannan ita ce ma’anar ‘yan’uwantaka ta haqiqa. Kuma wannan shi ne ma’anar xan’adamtaka."
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category