IBADU – GA MUSULMAI

IBADU – GA MUSULMAI

“Yayin da ka yi sujjada... komai yana komawa ne wurinsa”
To sau nawa ka xaga hannunka ba tare da ka ji cewar kana ganawa ne da Allah ba?

Sau nawa ka yi salla ta wuce kamar wani abu na al’ada, babu wani tasiri na samar da nutsuwa ko kwanciyar hankali a cikinta?

Ibada ba wai motsi ba ne kaxai da za ka kiyaye yin sa ba, a’a ita ibada kwantar da kai ne mai kyau, kuma wani lokaci ne na gaskata abin da ke tsaninka da mahaliccinka.

Yayin da ka saka goshinka a qasa,
Duka duniyar da take kewaye da kai sai ta zangwaye, sai ya zamana babu abin da ya rage daga kai sai Allah kaxai.

Allah ya ce:

“Ka karanta abin da ake yi maka wahayinsa na Alqur’ani, ka kuma tsai da salla; lalle salla tana hana alfasha da kuma abin qi. Kuma tabbas ambaton Allah shi ne mafi girma.” [Ankabut: 45]

Kowace da za ka yi raka’a horo ne a kan yin haquri,
Kuma kowace sujjada wanke zuciya ne daga qurar rayuwa.

Kuma yayin da kake ambaton Allah, Shi ma zai ambace ka ...
To a sannan ne za ka fahimci cewa, ibada ba wai kawai wajiba ba ce, a’a ni’ima ce aka yi maka.

Duk ibada ta gaske da ka yi tana sake jera hayaniyar da take cikinka,

Kuma tana tunatar da kai cewa: kai bawa ne, kuma wannan bautar ‘yanci ce.

A cikin sujjada ne hutu yake farawa.

326
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya