GAIBU DA BARZAHU
“Yayin da numfashi yake qoqarin qarewa”
Komai a cikin wannan rayuwar sai ka ga ya nufi hanyar qarewa.
Dariya da numfashi da qafafun da ake tafiya a kansu …. Duk sai ka ga suna nufatar hanyar yin shirun da ba mu san da shi ba.
Amma shin shirun shi ne qarshen lamari?
Alqur’ani yana ba mu labarin cewa a bayan wannan rayuwar akwai wata rayuwar ta daban.
Duniya ce da ba ma ganin ta, amma kuma ita tana jiranmu gaba xayanmu.
Allah yana cewa:
“Har sai idan da mutuwa ta zo wa xayansu zai ce: “Ubangijina, Ku mai da ni (duniya) mana. “Don in yi aiki na gari game da abin da na bari (a rayuwata).” Ina! Lalle wannan kalmace da yake faxin ta (da bakinsa). A gabansu kuwa akwai shamaki har zuwa ranar tashinsu.”.
A wannan lokacin ne ruhi yake rabuwa da gangar jiki, ba wai iya mutuwa ba ce, a’a tashi ne.
Tashi ne daga gafala zuwa yaqini.
A wannan wajen, babu waje ga masu voye fuskokinsu, kuma babu hujja ga gafalallu.
Sai dai kawai mutum ya farka ya ga gaskiyar da ya yi ta qaryatawa tsawon lokaci.
Ka yi tunani kaxan:
Shin a hankalce zai yiwu a halicce ka da irin wannan qwarewar sannan qarshenka ya zama babu abin da ya biyo bayansa?
Shin wannan hankalin da ruhi da jin daxi dukkansu babu manufa a samar dasu?
Rayuwar Barzahu ba tatsuniya ba ce, a’a alqwari ne daga Allah, kuma shi ne lokacin da mutum zai samu farkawa ta haqiqa
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category