Yanci Na Gaskiya A Cikin Alqur'ani

Yanci Na Gaskiya A Cikin Alqur'ani

Yayin da ka fahimci cewa, ‘yanci ba kishiyar imani ba ne
Allah Ta’ala yana cewa: “Babu tilastawa a addini”. [Baqara: 256]
Da yawa daga cikin mutane suna ganin kamar addinin yana yi wa mutum dabaibayi ya hana shi sakat.
Sai dai, shin samun ‘yanci yana nufin in rayu ba tare da wata manufa ba?
Shin samun ‘yanci yana nufin in mallaki komai, amma kada na mallaki kaina?
A cikin Alqur’ani, ‘yanci ba shi ne ka guje wa imani ba, a’a ‘yanci a cikin Alqur’ani shi ne ka samar wa da kanka hanya ta gaskiya a cikin yin imani.
Allah ba ya tilasta maka, sai dai yana kiranka ne.
Shi ya sa ma yake cewa: “Babu tilastawa a addini”.
Ga ta dai aya ce guda xaya, amma kuma ta isa ta canja dukkan wani yanayi.
Allah ba ya nufin ka qanqantar masa da kai saboda jin tsoro, sai dai saboda fahimtarka da abubuwa da kuma gaskiyarka.
Allah yana nufin ka da ka zavi hanya bisa ‘yancin zuciya.
Yayin da kake magana da Allah, ka yi magana irin ta wanda yake so a fahimce shi. Ka yi magana kamar wanda yake neman sanin wani abu a cikin hayaniya. Ka yi magana kamar wanda yake neman aminci ba wanda yake neman wata mu’ujiza ba
Ka yi magana kamar wanda yake so ya jiyar da tambayar da bai tava yi wa wani irinta ba.
Don haka ‘yanci a cikin Alqur’ani ba kishiyar imani ba ne, a’a abin da ake nufi da shi shi ne, ka yi imani alhali kana da ikon qin yin imanin. Sai kuma ka yi imanin saboda ranka ya yarda dashi.
To a sannan tafiya take farawa, tafiyar ruhi zuwa ‘yancinta na farko.

101
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya