Ya ku waxanda suka yi imani, an wajabta muku qisasi dangane."
Ya ku waxanda suka yi imani, an wajabta muku qisasi dangane da waxanda aka kashe; xa da xa, bawa da bawa, mace da mace[1]. To duk wanda aka yafe masa qisasin xan uwansa, to sai ya bibiye shi ta hanyar da ta dace, shi kuma ya biya diyyar ta hanyar kyautatawa. Wannan (abin da aka ambata), sauqi ne da rahama daga wajen Ubangijinku. Don haka duk wanda ya qetare iyaka bayan haka, to yana da azaba mai raxaxi
208
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category