Ta Ya Ya Alqur’ani Yake Magance Tsoro da Qunci Da Kuma Damuwa?
Tsoro wani abu da ake ji wanda kowanne daga cikinmu ya san shi.
Zai iya zuwa ba tare da wani sababi ba. Zai kuma iya zuwa ta dalilin wata kalma da za a furta ko wata matsaya da za a xauka, ko wani abu da za a tuna wanda ya jima ba a yi maganinsa ba.
Qunci shi ne wannan baqon mai nauyi da yake kutsawa cikin tunani yayin da ake cikin yanayi mafi rauni.
Damuwa kuwa ba za ta gushe tana bin mutum ba duk inda ya tafi.
Sai dai fa Alqur’ani ba zai bar ka da waxannan matsalolin ba, ba tare da ya baka magani game da su ba.
Yana ajiye maka wata kalma a gaba gareka da za ta sa komai ya lafa: “(Su ne) waxanda suka yi imani , zukatansu kuma suna nutsuwa da ambaton Allah. Ku saurara, da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa. [Ra’ad: 28]
Wannan ayar ba don a karantata ba ne kawai, tana siffanta haqiqanin xan’adamtaka ne da kuma ruhi.
Ba da qarfi zuciya take samun nutsuwa ba, haka ba da guduwa take samun sauqi ba, sai dai tana samun tabbatuwa yayin da ta ji cewa tana gaban Allah Ta’ala, amintacce wanda ake sauraro kuma ake fahimtarsa.
Alqur’ani yana magance tsoro yayin da yake qarfafa amintuwarka da Allah, yana kuma maganin qunci lokacin da yake tunatar da kai cewa, ba kai kaxai ba ne.
Hakanan yana maganin damuwa yayin da yake buxe maka qofar addu’a da qofar kyakkyawan fata da qofar haquri mai kyau.
Yayin da za ka kusanci Alqur’ani, yanayin da kake ciki ba zai canja ba a zahiri, sai dai ruhinka ne zai samu canji. Za ka wayi gari ka samu qarfi sama da wanda kake da shi a baya, ka samu nutsuwa sama da yadda kake tsammani, kuma ka samu qwarin gwiwar fuskantar abin da ka kasance kana tsoronsa a baya.
Ka xan nutsu kaxan, ka karanta aya xaya, ka xaga hannayenka ka ce: Ya Ubangijina.
Da sannu za ka gane cewa Alqur’ani ba ranaku kawai yake canjawa ba, a’a yana canja zuciyar da yake fuskantowa ne.
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category