Kira Don Yin Tuntuntuni Ba Tare Da Tsoro Ba

Kira Don Yin Tuntuntuni Ba Tare Da Tsoro Ba

Tuntuntuni ba Tare da Tsoro ba – Ga Wadanda ba Musulmi ba
Shin akwai ranar da ka taba jin wani labari...
Wanda ya sa ka kusa yin kuka, amma ba ka san dalilin hakan ba?
To irin wannan labarin, labari ne da yake magana da ruhinka ba da kunnuwanka ba.
Labari ne...wanda kamar da ma kana dakon zuwansa.
Wannan shi ne Alkur’ani.
Ba littafi ne da ake karantawa ba kawai...
Sai dai shi wani sako ne rayayye, da kake iya ji, kuma ka yi kuka, kuma ka rayu.
“(Allah) Mai rahama. Shi Ya koyar da Alkur’ani. Ya halicci mutum. Ya koyar dashi bayani.” [Arrahman: 1-4]
Alkur’ani ba littafin Musulmi ba ne kawai
Shi magana ce ga dukkan wani mutum.
Ga dukkan wanda ya yi tambaya: wane ne ni? Kuma don me nake rayuwa?
Kuma mece ce manufata a wannan duniyar?
Saboda me aka halicce ni? Me ya sa nake a nan? Kuma ina na dosa?
Ka karanta aya daya kawai...
Da nitsattsen sauti, da kuma budaddiyar zuciya...
Sannan ka tambayi kanka:
“Yanzu ba za su yi tunani na basira ba (game da) Alqur’ani ba, ko kuwa akwai wani rufi ne a kan zukatansu? [Muhammad: 24]
Kada ka tafiyar da mamakinka...kawai ka karanta, ka yi karatu
Kafin wani lokaci yazo...wanda ba za ka iya sauraron wani abu a cikinsa ba.

429
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya