Musulunci bai bar alakoki su tafi haka kawai ba tare da tsari ba...

Musulunci bai bar alakoki su tafi haka kawai ba tare da tsari ba...

Musulunci bai bar alakoki su tafi haka kawai ba tare da tsari ba...
A’a ya sanya musu ka’idoji da za a tsare rai da zuri’a da kuma mutunci.
Allah Ta’ala ya ce:
“An haramta muku auren iyayenku mata da ‘ya’yanku mata da ‘yan’uwanku mata da gwaggonninku da yagwalgwalanku da ‘ya’yan xan’uwa da ‘ya’yan ‘yar’uwa da iyayenku waxanda suka shayar da ku da ‘yan’uwanku mata ta wajen shayarwa, da iyayen matanku da agololinku waxanda suke cikin gidajenku, waxanda matan da kuka tava saduwa da su suka haife su, in kuwa ba ku tava saduwa da su ba, to babu laifi a kanku, da matan ‘ya’yanku maza waxanda suke na tsatsonku; haramun ne kuma ku haxa ‘yan’uwa mata biyu, sai dai abin da ya wuce a baya. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai jin qai. [Nisa’i: 23]
Wadannan ba wai iyakoki ne da aka sa haka kawai ba...a’a iyaka ce da take kare iyali daga rushewa.
Tana tsare jinane daga cakuduwa...tana kiyaye kauna daga rugujewa...yana tsare mutunci daga wargi.
Abin da Allah ya haramta..ba haramun ba ne kawai, a’a kariya ne da rahama da kuma tsara rayuwarmu.
Aure a Musulunci gini ne...ba sha’awa ce da take zuwa ta tafi kawai ba.
Saboda haka duk abin da aka hana... to akwai wata hikima mai zurfi a cikin hanin.
Abin da kuma aka halatta...to akwai yalwar da ta isa ta ba wa zuciya nutsuwa a cikinsa.

396
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya