Dan Adam A Cikin Alƙur'an
See other videos from same category
Yanzu mutum ba ya gani cewa Mu Muka halicce shi daga maniyyi, sai ga shi ya zama mai jayayya a fili?Ya kuma buga mana misali, kuma ya manta da halittarsa (yayin da) ya ce: “Wane ne zai raya qasusuwa, alhali kuma sun rududduge?Ka ce: “Wannan da Ya fare su tun farko Shi ne zai raya su; Shi kuwa Masanin kowacce irin halitta ne
Manzanni ne masu albishir kuma masu gargaxi, domin kada mutane su sami wata hujja a wurin Allah bayan aiko manzannin. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima
Shin yanzu wanda ya kasance matacce (kafiri), sai Muka rayar da shi, kuma Muka sanya masa haske (na shiriya), yana tafiya da shi cikin mutane, (yanzu) zai zama kamar wanda yake cikin duhu (na kafirci), ta yadda ba zai iya fita daga cikinsa ba? Kamar haka ne aka qawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa
Bukatuwar Mutane Zuwa Ga Wahayin Ubangiji
Kuma ka tuna sa’adda Ubangijinka Ya ce da mala’iku: “Lalle ni zan sanya wani halifa[1] a bayan qasa.” Suka ce: “Yanzu za Ka sanya mata wanda zai yi varna a cikinta kuma ya zubar da jini, alhali ga mu muna tasbihi tare da gode Maka, kuma muna tsarkake Ka?” (Allah) Ya ce: “Ni fa tabbas Na san abin da ku ba ku sani ba.”
Sai suka qaryata shi, sai Muka tserar da shi da waxanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwa, Muka kuma mayar da su masu maye gurbin (waxanda suka gabace su), Muka kuma nutsar da waxanda suka qaryata ayoyinmu. To duba ka ga yadda qarshen waxanda aka yi wa gargaxi ya kasance Sannan a bayansa (Annabi Nuhu) Muka aika manzanni zuwa ga mutanensu suka z...