Yanzu lokaci bai yi ba ga waxanda suka yi imani zukatansu su yi taushi da zikirin Allah da kuma abin da Ya saukar na gaskiya, kuma kada su zama kamar waxanda aka bai wa Littafi tun gabaninsu, sai lokaci ya tsawaita a gare su, sai zukatansu suka qeqashe; mafiya yawa kuma daga cikinsu fasiqai ne? [Hadid: 16]
Nawa nawa ne daga cikin zukata wadanda suka nesanta daga ambaton Allah ta’ala, har ya zamana sun yi sakayau sun kekashe.
Amma kiran Allah Ubangiji bai gushe ba yana kwankwasa kofar kira zuwa ga a dawo...
Yanzu lokaci bai yi ba ga waxanda suka yi imani zukatansu su yi taushi da zikirin Allah da kuma abin da Ya saukar na gaskiya, kuma kada su zama kamar waxanda aka bai wa Littafi tun gabaninsu, sai lokaci ya tsawaita a gare su, sai zukatansu suka qeqashe; mafiya yawa kuma daga cikinsu fasiqai ne? [Hadid: 16]
Gafala tana kekasar da zukata
Ambaton Allah kuma yana tausasata ya kuma sa ta yin sabuwar rayuwa.
Kada ka bari duniya ta tafiyar da kai_ka dawo yanzu-yanzu.
“Ka karanta abin da ake yi maka wahayinsa na Alqur’ani, ka kuma tsai da salla; lalle salla tana hana alfasha da kuma abin qi. Kuma tabbas ambaton Allah shi ne mafi girma. Kuma Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa.” [Ankabut: 45
Ana karanta Alkur’ani ne don a tsarkake rai
Salla kuma ana tsayar da ita ne don ta tsarkake yanayin mutum
Duk wanda ya kiyaye wurin yi wa Ubangijinsa salla, to za ta tsare shi daga karkacewa.
“Ka karanta abin da ake yi maka wahayinsa na Alqur’ani, ka kuma tsai da salla; lalle salla tana hana alfasha da kuma abin qi. Kuma tabbas ambaton Allah shi ne mafi girma. Kuma Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa.” [Ankabut: 45
Babu wani abin da ya fi ambaton Allah girma a duniya,
Domin shi ne hasken zuciya, kuma tsawatarwar rai, kuma tsanin samun tabbatuwa.
Duk lokacin da ka ambace shi (Allah) da gaskiya, to za ka zama ka kara samun kusanci dashi.
“Littafi ne mai albarka da Muka saukar maka da shi domin su yi tuntuntuni game da ayoyinsa, don kuma masu hankula su wa’azantu.” [Sad: 29]
Ba don ado da neman albarka aka saukar da Alkur’ani ba kawai,
A’a, sai dai an saukar da shi ne don mu fahimce shi, mu yi tuntuntuni game dashi, mu rayu a kan shiriyarsa a kan kowane irin gwadabe da muka bi.
Kuma lalle za Mu jarrabe ku da wani abin tsoro da yunwa da tawayar dukiya da ta rayuka da ta 'ya'yan itatuwa. Don haka ka yi albirshir ga masu haquri.” [Bakara: 155]
Jarabawoyi da Allah yake yi wa bayi, ba dalili ne da yake nuna fushin Ubangiji ba, a’a wata dama ce da masu hakuri suke samu don su daukaka.
Tsoro da yunwa da rashi....dukkansu darussa ne na kara samun yarda da Allah.
Kuma lalle za Mu jarrabe ku da wani abin tsoro da yunwa da tawayar dukiya da ta rayuka da ta 'ya'yan itatuwa. Don haka ka yi albirshir ga masu haquri.” [Bakara: 155]
“Ya ku waxanda suka yi imani ku nemi taimako ta hanyar haquri da salla. Lalle Allah Yana tare da masu haquri.” [Bakara: 153]
A yayin da al’amura suka tsananta, kada ka tafi neman mafita a wani wuri a karen fari, a’a ka nemi mafaka ta hanyar komawa zuwa ga hakuri da salla, a cikinsu akwai samun dauki daga sama.
“Ya ku waxanda suka yi imani ku nemi taimako ta hanyar haquri da salla. Lalle Allah Yana tare da masu haquri.” [Bakara: 153]
Allah ba ya barin wanda ya yi hakuri
A’a, yana kasancewa tare dashi yayin da yake cikin rauninsa da hawayensa, kuma a cikin kowace sujada akwai kyakkyawan fata.
“(Allah) Mai rahama. Shi Ya koyar da Alkur’ani. Ya halicci mutum. Ya koyar dashi bayani.” [Arrahman: 1-4]
Alkur’ani ya kasance shi ne ni’imar farko bayan rahama,
Kuma ya zama kamar mafi girman abin da za a koyar da mutum bayan an halicce shi...shi ne maganar Allah.
“(Allah) Mai rahama. Shi Ya koyar da Alkur’ani. Ya halicci mutum. Ya koyar dashi bayani.” [Arrahman: 1-4]
Allah shi ne wanda ya halicci mutum,
Kuma shi ne sanar da shi yadda zai yi magana ya isar da sako
Shin muna amfani da ni’imar bayani cikin abin da zai yardar dashi?
“Yanzu ba za su yi tunani na basira ba (game da) Alqur’ani ba, ko kuwa akwai wani rufi ne a kan zukatansu?” [Muhammad: 24
Alkur’ani ba littafi ne da ake karantawa ba kawai,
A’a, an saukar dashi ne don a yi tuntuntuni game dashi...don haka duk wanda bai yi tuntuntunin ma’anoninsa ba, to kamar akwai wani rufi a kan zuciyarsa wanda ba za a iya bude shi ba.
“Lalle wannan Alqur’anin yana shiryarwa ne ga (hanya) mafi miqewa, yana kuma yi wa muminai waxanda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa, lalle suna da lada mai girma.” [Isra’: 9]
Alkur’ani yana shiryar da kai zuwa hanya mafi mikewa,
Ba wai ta hanyar umarni da hani ba kawai, a’a a dukkan tsarin rayuwarka yana yi maka jagora zuwa ga rabauta da dacewa.
“Lalle wannan Alqur’anin yana shiryarwa ne ga (hanya) mafi miqewa, yana kuma yi wa muminai waxanda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa, lalle suna da lada mai girma.” [Isra’: 9]
Bushara mafi girma ga Muminai a cikin ‘yan kalmomi kawai take ba,
A’a, a cikin alkawarin Allah take ta hanyar samu lada babba ga wanda ya bi hanyar nagarta.
“Da Mun sanya shi Alqur’ani Ba’ajame da tabbas za su ce: “Me ya hana a bayyana ayoyinsa? Yanzu (a ce Alqur’ani) Ba’ajame (Annabi kuma) Balarabe?” Ka ce: “Shi ga waxanda suka yi imani shiriya ne da waraka. Waxanda kuwa ba sa yin imani akwai nauyi cikin kunnuwansu, shi kuma makanta ne a gare su.” Waxannan (sun yi kama da waxanda) ake kira daga wuri mai nisa.” [Fussilat: 44]
Alkur’ani bai takaita a kan wani yare ko wasu mutane ba,
A’a shi dai shiriya ne, kuma waraka ne ga dukkan wata zuciya mai yin imani,
Duk wanda ya kawar da kai ga barinsa, to wata tazara mai nisa za ta kasance a tsakaninsa dashi wadda ba za a iya kaiwa karshenta ba.
“Da Mun sanya shi Alqur’ani Ba’ajame da tabbas za su ce: “Me ya hana a bayyana ayoyinsa? Yanzu (a ce Alqur’ani) Ba’ajame (Annabi kuma) Balarabe?” Ka ce: “Shi ga waxanda suka yi imani shiriya ne da waraka. Waxanda kuwa ba sa yin imani akwai nauyi cikin kunnuwansu, shi kuma makanta ne a gare su.” Waxannan (sun yi kama da waxanda) ake kira daga wuri mai nisa.” [Fussilat: 44]
Zukata sune suke fahimta ba kunnuwa ba...
Wanda ya bude wa gaskiya zuciyarsa, to zai samu haske a cikin Akur’ani,
Wanda kuma ya rufeta, to ba zai taba saurara ba, ko da kuwa za a karanta masa ayoyi gaba dayansu.