Alkur’ani...Yayin da yake magana da ruhinka
Shin akwai ranar da ka taba sauraron wata magana...wadda ta sa ka kuka, amma kuma ba ka san dalilin hakan ba?
Magana ce da take zantawa da ruhinka, ba da kunnuwanka ba, magana ce wadda da ma kamar kana dakon zuwanta ne.
Wannan shi ne Alkur’ani
Ba littafi ne da ake karantawa ba kawai...
Sai dai shi wani sako ne da kake ji, ka ke kuma kuka saboda shi, kuma kake rayuwa saboda shi
“Lalle wannan Alqur’anin yana shiryarwa ne ga (hanya) mafi miqewa”. [Isra’: 9]
Shin ka taba jin cewa, dukkan wani abu dake daura da kai hayaniya ce...in ban da wannan sautin?
Sautin Alkur’ani...natsattse, mai tausasawa, amma kuma yana ratsa zuciya.
Ba wai kawai yana fada maka abin da ya zama dole ka aikata ba...
Sai dai ma yana sanar da kai ka san karan-kanka, kamar yadda ba ka fahimci kanka ba a baya.
Za ka zaci don kai aka rubuta sakon, duk da cewa an riga an rubuta shi karnuka da suka shude.
Za ka ji cewa yana abokantakarka yayin da ka kadaita.
Yana magana da kai lokacin babu wanda yake fahimtarka.
Yana lallashinka a lokacin da kake kuka a cikin dare.
Yana sa maka tabbatuwa yayin da kake cikin wani radadi..
Yana yi maka albishir yayin da kake cikin bakin ciki..
Yana baka karfi yayin da ka yi rauni...
Yana baka hakuri...yayin da zuciyarka ta gaji.
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category