Nadama Tana Farawa ne ta Dalilin Zavar

Nadama Tana Farawa ne ta Dalilin Zavar

Wasu daga cikin mutane suna zaton jivintar kafirai alaqa ce kawai wadda aka saba. Sai dai Alqur’ani yana bambanta tsakanin mu’amala da adalci da kyautatawa da kuma jivintar da za ta sa zuciya ta riqa yi musu biyayya, ko ta riqa gabatar da yardar su a kan yardar Allah, ko ta riqa taimakon su a kan varnar su. Wannan ne ma ya sa gargaxi ya zo a bayyane game da haka, inda Allah ya ce:
Ya ku waxanda suka yi imani, idan har kuka yi biyayya ga waxanda suka kafirta, to za su mayar da ku baya a kan dugaduganku, sai ku juya kuna hasararru.” [Ali Imran: 149]
Mutum yana tasirantuwa da wanda ya yarda da shi kuma yana yin koyi da shi, sai ta kai ga ya ji yana nisantar gaskiya taku bayan taku.
Sannan Alqur’ani yana suranta qarshen wannan hanya mai raxaxi da cewa:
“Kaicona ina ma ban riqi wane aboki ba”. [Furqan: 28]
Lallai wannan nadama ce wadda buri ba zai amfana da ita ba, yayin da ta bayyana ga mutumin da ya bi wasu a duniya cewa ba za su iya xaukar masa wani abu daga cikin laifukan da ya aikata ba a ranar alqiyama.
Don haka ka yi qoqari kaga cewa waxanda za ka jivinta su ne Allah da Manzonsa da kuma muminai. Kuma ka zavi wanda zai taimake ka a kan yi wa Allah biyayya. Saboda aboki hanya ce, jivintar wani kuma aqida ce, nadama kuma ba ta da amfani bayan dama ta suvuce.

5
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Drop Box )

Yi tarayya