Alkawurra da Gargadi
See other videos from same category
Wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qaga wa Allah qarya ko kuma ya qaryata gaskiya lokacin da ta zo masa? Yanzu ashe babu mazaunar kafirai a cikin Jahannama? Waxanda kuma suka yi jihadi saboda Mu to tabbas za Mu shiryar da su hanyoyinmu , kuma lalle Allah Yana tare da masu kyautatawa
Kyakkyawan Fatan da Kuma Tsoro
Yana shirya al’amari daga sama zuwa qasa sannan (al’amarin) ya hau zuwa gare Shi a cikin wani yini da gwargwadon (tsawonsa) yake shekara dubu ne daga abin da kuke qirgawa Wannan (Shi ne) Masanin voye da sarari, Mabuwayi, Mai rahama
Halittun da ba a gani
Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara ta musamman daga wajen Ubangijinku, da kuma Aljanna wadda faxinta yake daidai da sammai da qasa, an yi tanadinta domin masu taqawa (Su ne) waxanda suke ciyarwa a cikin halin yalwa da halin qunci, kuma masu voye fushi kuma masu yin afuwa ga mutane. Allah kuwa Yana son masu kyautatawa
Kuma al’amarinmu bai zamanto ba face kalma xaya kamar qiftawar idoHaqiqa kuma Mun hallakar da ire-irenku , to ko akwai mai wa’azantuwa?Kuma kowane abu da suka aikata yana cikin littattafaiKowane qaramin abu da babba kuma suna nan a rubuceLalle masu taqawa suna cikin gidajen Aljanna da qoramu