Tsare Amana Tsare Rayuwa Ne
See other videos from same category
Kuma sakamakon mummunan (abu) shi ne mayar da mummuna kamarsa; to wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata, to ladansa yana wurin Allah. Lalle Shi ba Ya son azzalumai
Waxanda suka kyautata aiki suna da sakamako mafi kyau (watau Aljanna) da kuma qari. Wani qunci da qasqanci kuma ba za su same su ba. Waxannan su ne ‘yan Aljanna; su masu dawwama ne a cikinta
Kada kuma ka yi tafiya a bayan qasa kana mai girman kai; lalle kai ba za ka tsaga qasa ba (don qasaita) kuma ba za ka kai tsawon duwatsu ba
Da yawa daga cikin ma’abota littafi sun yi burin ina ma a ce su mayar da ku kafirai bayan imaninku, saboda hassada daga zukatansu, bayan kuma gaskiya ta bayyana a gare su. Don haka ku yi afuwa ku kawar da kai har sai Allah Ya zo da al’amarinsa. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai
Farin Cikin Haquri
alle masu taqawa suna cikin inuwoyi da idanuwan ruwaDa kuma ababan marmari daga abin da suke sha’awaKu ci kuma ku sha kuna masu farin ciki saboda abin da kuka kasance kuna aikatawaLalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa