Tsare Amana Tsare Rayuwa Ne
See other videos from same category
Waxanda suka kyautata aiki suna da sakamako mafi kyau (watau Aljanna) da kuma qari. Wani qunci da qasqanci kuma ba za su same su ba. Waxannan su ne ‘yan Aljanna; su masu dawwama ne a cikinta
To wanda ya ba da (haqqoqin da ke kansa) ya kuma yi taqawaYa kuma gaskata (sakamako) mafi kyauTo lalle ne za Mu sauqaqa masa (hanyar) AljannaAmma kuma wanda ya yi rowa (da haqqin Allah) ya kuma wadatu (da neman lada)Kuma ya qaryata (sakamako) mafi kyauTo lalle ne za Mu hore masa (hanyar) wuta
Bayin (Allah) Mai rahama kuwa (su ne) waxanda suke tafiya a bayan qasa a natse; idan kuma wawaye sun yi musu magana (sai) su faxa (musu) magana ta aminci
Farin Cikin Haquri
Kuma sakamakon mummunan (abu) shi ne mayar da mummuna kamarsa; to wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata, to ladansa yana wurin Allah. Lalle Shi ba Ya son azzalumai
Kada kuma ka yi tafiya a bayan qasa kana mai girman kai; lalle kai ba za ka tsaga qasa ba (don qasaita) kuma ba za ka kai tsawon duwatsu ba