Bukatuwar Mutane Zuwa ga Albarka

Bukatuwar Mutane Zuwa ga Albarka

Albarka ni’ima ce daga Allah Mai girma da daukaka, yana bayar da ita ga wanda ya ga dama. Kuma albarka tana daga cikin abubuwan da dan’adam yake bukatarsu a rayuwarsa. Da yawa daga cikin mutane suna lura game da tawayar albarka a dukiyoyinsu da lokutansu, wani lokaci ma a lafiyarsu da iyalinsu, duk da kokarin da suke yi na samar da abubuwan da ake bukata a rayuwa. Albarka ba ita ce samun madudiyar dukiya ko rayuwa mai tsawo ba kawai, a’a, albarka ita ce, samun kari da habaka a cikin dukkan komai, kuma tana kasancewa ne a cikin dacewar da Allah Ta’ala yake sa wa a cikin rayuwa, wanda zai sa ka ga aiki kadan, amma kuma yana dauke da babban lada, hakanan arziki kadan amma kuma dawwamamme, ko kuma samun cikakkiyar lafiya tare da cewa shekaru sun tura sun tafi.
Allah Ta’ala yana cewa:
Kuma in da a ce mutanen alqaryu sun yi imani kuma sun tsare dokokin Allah, to lalle da Mun buxe musu albarkatu daga sama da kuma qasa, sai dai sun qaryata, Mu kuwa sai Muka kama su da abin da suka kasance suna aikatawa. [A’araf: 96]
Wannan ayar tana bayyana cewa, albarka tana samuwa ne ta dalilin imani da tsare dokokin Allah. Don haka idan mutum ya kasance ya kusanci Allah, to duk abin da zai aikata zai kasance mai cike da albarka, tare da haka kuma akwai budi na alheri daga Allah Mai girma da daukaka ta sama da kasa.
Da yawa daga cikin mutane suna kukan karancin albarka a cikin rayuwarsu, hakanan a cikin
dukiyoyinsu da lokutansu, tare da cewa suna cikin ni’ima da ake gani a zahiri. Don haka daga cikinsu akwai wanda yake da dukiya amma ba ya ciyar da ita bangarorin alheri. Don haka za ka ganshi yana ta lissafinta tsawon lokaci, yana tafiyar da tunaninsa a kanta, ba tare da ya samu wani hutu ko albarka ba a cikinta. Wani kuma yana tafiyar da dukiyarsa ne cikin ayyukan sabon Allah, wanda hakan ke ninka masa wahalarsa, ya kuma rasa albarka a arzikinsa.

400
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya