Kyawawan Halaye."
Xabi’u ba yaren addini ba ne ba kaxai, a’a xabi’u yare ne na xan’adamtaka.
Za ta iya kasancewa ba ka san komai ba game da imani. Amma kuma tare da haka za ka iya sanin ma’anar rahama da tausasawa da afuwa.
Ka yi shiru kafin ka cutar da wani
Ka saurari magana kafin ka yi hukunci game da ita.
Ka yi murmushi yayin da wani yake niyyar yin fushi.
Alqur’ani yana tunatar da mu faxin Allah: “Kuma ka tuna lokacin da Muka xauki alqawari daga Banu Isra'ila cewa, ba za ku bauta wa kowa ba sai Allah, kuma za ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da miskinai, kuma ku riqa yi wa mutane kyakkyawar magana, kuma ku tsai da salla, kuma ku ba da zakka, sannan sai kuka ba da baya sai 'yan kaxan daga cikinku, alhalin kuna masu bijirewa.” [Baqara: 83]
Magana mai kyau, aiki mai sauqi da kuma zuciyar da ba a yi wa rauni ba.
A yau duniya a cike take da hayaniya, sai dai rayuka suna buqatar samun nutsuwa.
Duk wani daddaxan aiki qarami, hakanan duk wani murmushi, sannan duk wata kalma ta nuna tausayi, waxannan abubuwa suna barin wani tasirin da ba a ganinsa, amma kuma suna gina wasu irin gadoji a tsakanin zukata.
Don haka ka zamo wata alama mai tausasawa, ko da kuwa duniya ta bayyana a matsayin qeqasasshiya. Idan ka yi haka za ka samu cewa, wannan tausasawar ta dawo maka da ninkin-ba-ninkin abin da ka yi."
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category