Alkawurra da Gargadi
See other videos from same category
Kyakkyawan Fatan da Kuma Tsoro
Waxanda suka zauna a gida daga cikin muminai ba su fita yaqi ba, in dai ba masu larura ba, ba za su yi daidai da masu jihadi don xaukaka kalmar Allah da dukiyoyinsu da kawunansu ba. Allah Ya fifita darajar masu jihadi da dukiyoyinsu da kawunansu a kan waxanda suka zauna a gida. Kuma dukkansu Allah Ya yi masu alqawarin Aljanna. Kuma Allah Ya fifita...
Lalle Allah Ya sayi rayuka da dukiyoyin muminai daga wurinsu cewa suna da Aljanna: Za su yi yaqi saboda Allah, sai su kashe su ma kuma a kashe su. Alqawari ne na gaskiya da Ya xaukar wa kansa a cikin Attaura da Linjila da Alqur’ani. Wane ne ya fi Allah cika alqawarinsa? Saboda haka sai ku yi farin ciki da cinikin nan naku da kuka yi da Shi. Wannan...
Yin Aiki Tukuru da Kokari
Ubangijinku kuma Ya ce: “Ku roqe Ni zan amsa muku. Lalle waxanda suke yin girman kai game da bauta min, ba da daxewa ba za su shiga Jahannama a wulaqance.” Allah ne wanda Ya halitta muku dare don ku natsu a cikinsa, rana kuma don ku ga (yadda za ku yi harka). Lalle Allah Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa
Yana shirya al’amari daga sama zuwa qasa sannan (al’amarin) ya hau zuwa gare Shi a cikin wani yini da gwargwadon (tsawonsa) yake shekara dubu ne daga abin da kuke qirgawa Wannan (Shi ne) Masanin voye da sarari, Mabuwayi, Mai rahama