Zargi Da Cin Zarafin00
See other videos from same category
Shin kuwa ka ga wanda ya xauki son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, Allah kuwa Ya vatar da shi a kan yana sane[1], Ya kuma rufe jinsa da zuciyarsa, kuma Ya sanya yana a kan ganinsa, to wane ne zai shiryar da shi in ba Allah ba? Me ya sa ba kwa wa’azantuwa?
Zalunci Duhu Ne00
Lalle Allah Yana umarni da yin adalci da kyautatawa da kuma bai wa makusanta (taimako), Yana kuma hana alfasha da mummunan aiki da zalunci. Yana gargaxin ku don ku wa’azantu
Ka ce (da su): “Ba na ba ku labarin waxanda suka fi asarar ayyukansu ba?“(Su ne) waxanda aikinsu ya vace a rayuwarsu ta duniya alhali kuwa su suna tsammanin suna kyautata aiki ne.”Waxannan (su ne) waxanda suka kafirce wa ayoyin Ubangijinsu da kuma gamuwa da shi, sai ayyukansu suka lalace, ba za Mu sanya musu wani ma’auni ba a ranar alqiyama
Zan kautar da waxanda suke yin girman kai a bayan qasa ba tare da haqqi ba daga (fahimtar) ayoyina; idan kuma za su ga kowace irin aya ba za su yi imani da ita ba, idan kuma da za su ga hanyar shiriya ba za su riqe ta hanyar bi ba, (amma) idan kuwa za su ga hanyar vata, to za su riqe ta hanyar bi. Wannan kuwa saboda sun qaryata ayoyinmu, kuma sun k...
Lalle sakamakon waxanda suke yaqar Allah da Manzonsa, kuma suke varna a bayan qasa[1], shi ne kawai a karkashe su ko kuma a giggicciye su ko kuma a yayyanke hannayensu da qafafuwansu a tarnaqe ko kuma a kore su daga qasa. Wannan qasqanci ne a gare su a nan duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma