Wane ne Yake Salla a Kusa da kai
Za ta iya yiwu wa wani sanannen mutum ya yi salla a kusa da kai, ka san fuskar sa, amma kuma ba ka san sunansa ba.
Za ta iya yiwu wa ka san Garin da ya zo daga gare shi, amma kuma ba ka san mene ne ke sa zuciyar shi farin ciki ko kuma mene ne yake xauke masa hankali ba.
A cikin salla yana tsayuwa da kai kafaxa da kafaxa, shin za ka iya bashi dama ka yi magana tare da shi?
Allah Ta’ala yana cewa: “Ya ku mutane, lalle Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, Muka kuma sanya ku al’ummu da qabilu don ku san juna. Lalle mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku taqawa. Lalle Allah Masanin sarari ne, Masanin voye.” [Hujurat: 13]
Bayan idar da sallar da za a yi nan gaba, ka xan tsaya kaxan.
Ka yi masa sallama, ka tambaye shi ka ji ya ya yake.
Ka tsaya ka saurara ba tare da ka mayar da hankali kan yaren shi ya zama shi ne gundarin dalilin haxuwar ku ba.
A sannan ne za ka gane akwai wani abu da ya ba wa muhimmanci wanda ya yi kama da irin wanda ka ba wa muhimmanci. Ko kuma ka ji wani labari wanda ba ka tava jin irinsa ba.
Ba ka buqatar sai labarin ku ya zo iri xaya kafin ku qulla abokantaka ta qauna a tsakanin ku.
Zai iya yiwu wa abokantaka tagari ta fara daga yin sallamar da ba a yi gaggawar rabuwa ba bayan an yi ta.
Related Videos
See other videos from same category