Al Qur'ani Da Ci Gaban Al Ummah
See other videos from same category
Lalle waxanda suke kafirce wa Allah da manzanninsa, kuma suke nufin su nuna bambanci tsakanin Allah da manzanninsa, kuma suna cewa: “Mun yi imani da wasu, mun kuma kafirce wa wasu,” kuma suna son su riqi wani tafarki tsakanin wannan (imani da kafirci) Waxannan su ne kafirai na haqiqa. Kuma Mun yi wa kafirai tanadin wata azaba mai wulaqantarwa
Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya, kada kuma ku rarraba. Kuma ku tuna ni’imar Allah da Ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya haxa tsakanin zukatanku, sai kuka zamo ‘yan’uwan juna a sakamakon ni’imarsa, a da kuma kun kasance a kan gavar ramin wuta sai Ya tserar da ku daga gare ta. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyin...
ALIF LAM RA. Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya
Ya ku waxanda suka yi imani, an wajabta muku qisasi dangane da waxanda aka kashe; xa da xa, bawa da bawa, mace da mace[1]. To duk wanda aka yafe masa qisasin xan uwansa, to sai ya bibiye shi ta hanyar da ta dace, shi kuma ya biya diyyar ta hanyar kyautatawa. Wannan (abin da aka ambata), sauqi ne da rahama daga wajen Ubangijinku. Don haka duk wanda...
Allah ne wanda Ya hore muku kogi don jiragen ruwa su riqa gudu a cikinsa da umarninsa, don kuma ku nema daga falalarsa don kuma ku gode
Lalle wannan Alqur’anin yana shiryarwa ne ga (hanya) mafi miqewa, yana kuma yi wa muminai waxanda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa, lalle suna da lada mai girma