Qanqan da Kai (Tawalu’u)."

Qanqan da Kai (Tawalu’u)."

Ka xan yi tunani na xan lokaci kaxan kafin ka kwanta bacci.
Nutsuwa tana lulluve wurin…sannan saman dake samanka ta yi fayau.
Allah ya sanya marfi a kan zuciyarka, kamar yadda dare yake lallube duniya da duhunsa.
Wane ne kai, in ba da rahamarsa ba?
Wane ne kai, shin ka manta kai bawa ne, mai rauni kuma mabuqaci?
Wani lokaci girman kai yana farawa a hankali a hankali.
Ba zai fito fili ya kwaza hakan ba, sai dai zai riqa yin gunguni a ransa cewa:
“Ni na fi waxansu,” “Na cancanci sama da haka”, “Sanina ya fi haka”.

Shi kuma Alqur’ani yana yi mana raxa cikin hikima cewa: “Bayin (Allah) Mai rahama kuwa (su ne) waxanda suke tafiya a bayan qasa a natse; idan kuma wawaye sun yi musu magana (sai) su faxa (musu) magana ta aminci”. [Furqan: 63]
Cewa suna tafiya a natse, wannan ba rauni ba ne, a’a alamar hankali ce.
Kuma suna sane da cewa duk abin da suka mallaka kyauta ce daga Allah.
Wannan ya haxa da abincin da suke ci, da iskar da suke shaqa, hatta samun damar da suka yi ta yin sujjada, kai ba ma haka ba dukkan wani abu da suke da shi kyauta ce daga gare shi.
Qanqan da kai ba shi ne ka qasqantar da kanka a gaban mutane ba, qanqan da kai shi ne ka riqa tuna wane ne kai a gaban Allah Ta’ala.
Duk lokacin da zuciya ta risina, to ruhi yana samun xaukaka.
Duk lokacin da ka yi tafiya cikin nutsuwa, to za ka ji ka samu kusanci da Allah Mai rahama.
Yayin da za ka qosar da ranka da qanqan da kai (tawalu’u), to hasken da ke cikin ranka zai qaru, ya zamana ya haskaka maka duk inda ka nufata."

43
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya