Ya Kuma Same ka Marashin Shiriya Ya Shiryar (da kai) ."

Ya Kuma Same ka Marashin Shiriya Ya Shiryar (da kai) ."

Ya Kuma Same ka Marashin Shiriya Ya Shiryar (da kai) – Don Musulmi
Allah yana cewa: “Ya kuma same ka marashin shiriya, Ya shiryar (da kai).
Yayin da ake cikin yanayin aikata zunubi da yanayin rauni da taqaitawa a cikin ayyuka na gari, za ka iya zaton cewa hanyar ta riga ta qare, kuma kai ba ka cancanci samun shiriya ba.
Sai dai ya kamata ka yi la’akari da abin da Allah ya faxa wa Annabinsa (S.A.W) na cewa: “Ya same ka marashin shiriya Ya shiryar (da kai).
Idan har shiriya ta kasance ga mafi alherin mutane wanda ada ba ya kanta bai san wahayi ba, to ta ya ya kuma ba za ta kasance tare da kai ba?
Allah ba ya shiryarwa saboda mun cancanci a shiryar da mu, sai dai don saboda kasancewarsa mafi jin qan masu jin qai.
Duk yadda kake ganin ka nisanta ga barin shiriya, to in dai kana yin bincike game da gaskiya, to shiriya na nan tana jiranka.
Ka buxe mus’hafi, ka karanta shi da gaskiya.
Zai iya kasancewa farkon ayar da za ka fara haxuwa da ita, ita ce qofar farko da za a buxe maka daga sama.

13
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya