See other videos from same category
Kuma akwai wasu mutane waxanda suke bauta wa wasu kishiyoyi ba Allah ba; suna son su kamar son Allah; waxanda kuwa suka yi imani sun fi son Allah (fiye da komai). Da a ce waxanda suka yi zalunci za su ga lokacin da suke ido huxu da azaba (to da sun gane) cewa, lalle duk wani qarfi na Allah ne gaba xaya, kuma lalle Allah Mai tsananin azaba ne
Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar wa kowace al’umma da mai ba da shaida a kansu daga jinsinsu, Mu kuma zo da kai (Annabi Muhammadu) shaida a kan waxannan (wato al’ummarka). Kuma Mun saukar maka da Littafi ne (wato Alqur’ani) don bayani ga kowanne abu, kuma shiriya da rahama da bushara ga Musulmi
“Lalle ni kam na juyar da fuskata ga Wanda Ya halicci sammai da qasa, ina mai kauce wa varna kuma ni ba na cikin masu yin shirka.”
k
Kissoshin Shiriya a Cikin Alƙur ani
Yanzu mutum yana tsammanin za a bar shi haka sasaka ? Shin bai kasance wani xigo na maniyyi da ake zuba shi (a mahaifa) ba? Sannan ya zama gudan jini sannan (Allah) Ya halicce (shi) sai Ya daidaita (shi)?