Bautar Wanin Allah Ita ce Zunubi Mafi
Allah ya halicci mutum don ya bauta masa shi kaxai. Shi ya sa ya kasance mafi girman haqqin Allah a kan bayinsa shi ne su kaxaita shi da bauta, hakanan su kaxaita shi da addu’a da fata da tsoro da yanka da bakance da sauran nau’ukan ibada.
Sai dai shirka tana farawa ne daga lokacin da mutum ya juyar da xaya daga cikin waxannan ibadun zuwa ga wanin Allah, yana mai qudurce cewa wanin Allah yana mallakar amfanarwa ko cutarwa ko kuma ya qudurce cewa akwai wanda ya cancanci a roqe shi kamar yadda ake roqar Allah Ta’ala.
Haqiqa Alqur’ani ya bayyana haqiqanin waxanda suke bautawa wani ba Allah ba, inda ya ce:
“Suka kuma riqi wasu ababen bauta ba Allah ba, don a taimaka musu. Ba za su iya taimakon su ba, su da gumakan nasu duka ababen tattarawa ne (cikin wuta).”. [Yasin: 74-75]
To wanda ba zai iya taimakawa kansa ba, ta ya ya za a nemi biyan buqata ko yaye damuwa daga wurinsa?
Kuma kaxaita Allah da bauta ba kalma ce da ake furtawa a baki ba kawai, a’a, tauhidi shi ne tsarkake zuciya da yin aiki don Allah shi kaxai, kada a kira kowa in ba Allah ba, kada a yi fatan wani abu in ba a wurin sa ba, kada a fuskantar da wata ibada in ba ga shi kaxai ba Allah Mai girma da xaukaka.
Kuma duk wanda ya tsare tauhidin sa, to haqiqa ya yi riqo da abu mafi girma da zai tseratar da shi a duniya da lahira.
النص
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category