See other videos from same category
Ya ku waxanda aka bai wa Littafi, haqiqa Manzonmu ya zo muku, yana bayyana muku da yawa daga cikin abin da kuke voyewa daga Littafin, yana kuma yin afuwa ga abubuwa da dama daga ciki. Haqiqa haske ya zo muku daga Allah, da kuma Littafi mai bayyanawa Da shi ne Allah Yake shiryar da wanda ya bi yardarsa hanyoyi na aminci, kuma Yake fitar da su daga...
ALIF LAM RA . Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya
Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari, to (Allah) Mai rahama zai sanya musu qauna
Sai Musa ya jefa sandarsa, sai ga ta tana lanqwame duk abin da suke qagowa (na sihiri) Sai aka durqusar da masu sihirin suna masu sujjada Suka ce: “Mun yi imani da Ubangijin talikai
Ta Ya ya Alƙur ani Yake Shiryar da Ruɗaɗɗu
Kuma kamar haka ne Muka yiwo maka wahayin Ruhi (watau Alqur’ani) daga umarninmu. Ba ka zamanto ka san mene ne littafi ko kuma imani ba, sai dai kuma Mun sanya shi (Alqur’ani) haske ne da Muke shiryar da wanda Muka ga dama daga bayinmu da shi. Lalle kuma kai tabbas kana shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici