VARNA DA ABUBUWA MASU HALAKARWA

VARNA DA ABUBUWA MASU HALAKARWA

“Yayin da zuciya ta mutu”
A cikin kowane mutum akwai wani sauti da yake bambance tsakanin gaskiya da qarya.

Sauti ne da ba a jin shi da kunne, amma yana sanya raxaxi a zuciya idan muka sava masa.

Sai dai duk lokacin da wannan sautin ya yi shiru, to a lokacin ne rushewa ta fara aukuwa.

A wayi gari ana ganin qarya a matsayin qwarewa, a riqa kiran zalunci da qarfi,

A riqa gabatar da abin kunya a matsayin ‘yanci,

haka kuma za a canja ma’anar komai
kuma haske da duhu su cakuxe.

Allah yana cewa:
“Varna ta bayyana a kan tudu da kuma (cikin) ruwa saboda abubuwan da hannayen mutane suka aikata don a xanxana musu sashin abin da suka aikata, ko wataqila sa juyo.” [Rum: 41]


Yayin da imani yake voyewa, to babu ma’aunin da zai yi saura.

Kowace doka ana canja ta ne daidai da son zuciya, kowace zuciya kuma tana neman abin da zai yi mata daxi ne ba ruwanta da makomar da za ta tsinci kanta a ciki.

Sai dai shi addini ba dabaibayi ne ga ‘yanci ba, sai dai shi wata katanga ce da take kare mutum daga birkixewa ya zama kamar wata dabbar daji.

Musulunci yana dawo wa da zuciya sautinta, ya kuma dawowa da mutum karamarsa.

Ka xan yi tunani kaxan:
Shin ‘yanci shi ne ka yi abin da ka ga dama?

Ko kuma ‘yanci shi ne ka yi abin da zai yardar da Ubangijinka?
Wataqila ‘yanci na gaske zai fara... lokacin da muka koma zuwa ga Allah.

297
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya