(Ka tuna) kuma lokacin da Muka juyo maka da wata jama’a."
(Ka tuna) kuma lokacin da Muka juyo maka da wata jama’a ta aljannu don su saurari Alqur’ani[1]. To lokacin da suka halarto shi, sai suka ce: “Ku yi shiru;” sannan lokacin da aka gama (karatunsa) sai suka juya zuwa mutanensu suna yi musu gargaxi
Suka ce: “Ya ku mutanenmu, haqiqa mu mun jiwo wani littafi da aka saukar bayan Musa, mai gaskata abin da yake gabaninsa, yana shiryarwa zuwa gaskiya da kuma zuwa tafarki madaidaici
589
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category