Al Qur'ani Da Ci Gaban Al Ummah
See other videos from same category
Lalle waxanda suke kafirce wa Allah da manzanninsa, kuma suke nufin su nuna bambanci tsakanin Allah da manzanninsa, kuma suna cewa: “Mun yi imani da wasu, mun kuma kafirce wa wasu,” kuma suna son su riqi wani tafarki tsakanin wannan (imani da kafirci) Waxannan su ne kafirai na haqiqa. Kuma Mun yi wa kafirai tanadin wata azaba mai wulaqantarwa
Lalle wannan Alqur’anin yana shiryarwa ne ga (hanya) mafi miqewa, yana kuma yi wa muminai waxanda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa, lalle suna da lada mai girma
Allah kuwa Ya yi wa waxanda suka yi imani daga cikinku suka kuma yi aiki na gari alqawarin lalle zai sanya su halifofi a bayan qasa kamar yadda Ya sanya waxanda suke gabaninsu halifofi, kuma lalle zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, tabbas kuma zai dawo musu da zaman lafiya bayan zamantowarsu cikin tsoro. Su bauta mini, ba sa yin s...
Bambanci Tsakanin Maganin Al Qur'ani Da Maganin Yammacin Don Matsalolin Al'umma
Ya kai wannan Annabi, faxa wa matanka da ‘ya’yanka mata da kuma matan muminai (cewa) su sanya lulluvinsu. Wannan shi ya fi sanya wa a gane su, don kada a cuce su. Allah kuma Ya kasance Mai gafara ne, Mai rahama
ALIF LAM RA. Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya