Sulhu Tsakanin Mutane
See other videos from same category
Yanzu waxanda suka kafirta ba sa ganin cewa a da can sammai da qasa a haxe suke, sannan Muka raba su[1]; Muka kuma halicci duk wani abu mai rai daga ruwa? To me ya sa ba za su yi imani ba?
Kuma Allah Ya halicci kowace dabba daga ruwa; sannan daga cikinsu akwai waxanda suke jan ciki, kuma daga cikinsu akwai waxanda suke tafiya a kan qafa biyu, akwai kuma waxanda suke tafiya a kan qafa huxu. Allah Yana halittar abin da Ya ga dama. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai
“Wanda kuma ya bijire wa Alqur’ani to lalle zai yi rayuwa mai qunci, kuma Mu tashe shi makaho ranar alqiyama.”
Kuma da Ubangijinka Ya ga dama da lalle Ya yi mutane al’umma xaya (a kan addini xaya). Ba kuwa za su gushe suna masu savawa juna ba
Ya ku waxanda suka yi imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa Kuma ku yi tasbihi a gare Shi safe da yamma
Kuma (ka tuna) lokacin da Ubangijinka ya ce da mala’iku: “Lalle Ni zan halicci mutum daga busasshen tavo mai amo na wani yumvu mai wari