Maryamu…Mace ce da Allah ya Zava

Maryamu…Mace ce da Allah ya Zava

Za ta iya yiwuwa ka san Nana Maryam ne daga labarin haihuwarta. Hakanan kuma zai iya yiwuwa ka fara jin sunan ta ne tun kana xan qaramin ka. Sai dai shin ka san yaya Alqur’ani yaya riqa magana game da ita? Alqur’ani bai fara magana a kanta da jayayya ko da savanin da yake a tsakanin addinai ba, sai dai ya fara magana game da ita ne da girmamawa da kuma magana a kan matsayin ta a wurin Allah Ta’ala.
Allah Ta’ala yana cewa Kuma ka tuna lokacin da mala’iku suka ce Ya ke Maryamu, lalle Allah Ya zave ki, Ya kuma tsarkake ki, kuma Ya zave ki a kan sauran mata na talikai Ali Imran: 42]
Kalmomi ne ‘yan kaxan, sai dai kuma suna xauke da ma’ana mai girman gaske, ma’anar da ta qunshi; Zavi da tsarkaka da matsayi na musamman. Sunan Maryam a cikin Alqur’ani ba suna ne da yake zuwa ya wuce ba kawai ba tare da wata ma’ana ba. A’a suna ne na macen da aka sani da imani da ibada da gaskiya har ya zamana an samu Sura sukutum da take xauke da sunan ta, wato; Suratu Maryam.
Abin dubawa a nan shi ne yayin da Alqur’ani yake ba da labarin ta, ba ya ba da labarin ta a matsayin wata mace da ta sha bamban da mutum, a’a yana bayar da labarin ta ne a matsayin ta na mace wadda ta rayu da imani da tsoron Allah da samun jarrabawa da kuma yarda da Allah. Za ta iya yiwuwa ka san qissar ta a baya, amma dai Alqur’ani yana kiran ka da qara sauraron qissar ta kamar yadda ya ba da labarin ta.


11
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya