Wane ne Ya fi kyakkyawar Magana Fiye da Wanda Ya yi Kira Zuwa ga Allah."

Wane ne Ya fi kyakkyawar Magana Fiye da Wanda Ya yi Kira Zuwa ga Allah."

Kira zuwa ga Allah Mai girma da daukaka yana daga cikin mafi kololuwar ayyukan da ya kamata Musulmi ya mayar da hankalinsa a kansa. Kira zuwa ga Allah shi ne kira zuwa ga kyawawan dabi’u, da kyakkyawar mu’amala da kiyaye hakkoki, da tsayar da adalci a tsakanin mutane. Ta hanyar wannan kiran ne ‘yan’uwantaka da soyayya za su samu tabbatuwa a tsakanin Musulmi, kuma ta hanyarsa ne cikakken zaman lafiya da kammalallen tsari za su yi jagoranci irin wanda zai dace da shari’ar Allah Ta’ala.
Wannan zaman lafiyar bai takaita a kan zaman
lafiyar al’umma ba kawai, a’a ya hado har da samun zaman lafiyar rai da ruhi na al’ummar Musulmi. Ta yadda munanan dabi’u da suke kawo wa hadin al’umma cikas za su gushe. Hakanan ta hanyar samar da wannan kiran ne gaskiya take bayyana, hikidi ko kullaci kuma ya gushe, a samu kuma karancin sabani a tsakanin mutane.
Kira zuwa ga Allah bai takaita a kan magana da baki ba kawai, a’a ya hada har da aiki nagari da niyya tsarkakka yayin yada aikin alheri, da tsayar da farillan addini da hakkokin al’umma bisa hali mafi cika. Mai yin kira zuwa ga Allah shi ne wanda yake kokari wurin yada kyawawan dabi’un Musulunci madaukaka, wadanda suke tsara rayuwar mutane ta kowane bangare, wanda ya hada da kyakkyawar mu’amala da salla da zakka. Hakanan mu’amalolin kasuwanci da na al’umma sun dogara ne a kan amana da aminci.
Hakika ayoyin Alkur’ani masu yawa sun zo wadanda suke kwadaitarwa a kan kira zuwa ga addinin Allah Ta’ala, wanda hakan ke bayyana girman wannan aikin, daga cikin wadannan ayoyi akwai fadin Allah Ta’ala: “Wane ne Ya fi kyakkyawar Magana Fiye da Wanda Ya yi Kira Zuwa ga Allah ya kuma yi aiki nagari, kuma ya ce, “Lalle ni ina daga cikin Musulmi” [Fussilat:33]
Wannan ayar tana bayyana cewa, kira zuwa ga addinin Allah shi ne mafi girman magana da za a yi a bayan kasa, tana kuma nuna ita ce mafi girman kalmar da ya kamata mutum ya furta, saboda ta hada tsakanin kira zuwa ga addini da kuma aiki nagari, sannan kuma tana kiran mutum zuwa ga ya zamanto abin koyi a aikinsa kamar yadda yake a maganarsa.
Kira zuwa ga addinin Allah ba aiki ne na daidaikun mutane ba kawai, a’a aiki ne na kowa da kowa, kuma wajibi ne a kan al’ummar Musulmi. Wajibi ne da yake bukatar taimakekeniya da tsari a tsakanin Musulmi domin isar da sakon Musulunci ga wasu, sawa’un Musulmi ne ko ba Musulmi ba. Dalilai da dama a cikin Alkur’ani da sunnar Annabi (S.A.W) sun tabbatar da wajabcin yin kira zuwa ga addinin Allah Mai girma da daukaka. Dalilan da suke nuna cewa, yin kiran Fard kifaya ne a kan al’umma, ta yadda idan wasu suka tsayu dashi, to wajabcin ya fadi a kan sauran al’umma. Amma tare da haka yin da’awar yana cikin sunna mai karfi a hakkin sauran al’ummar. Da’awa tana a matsayin sako mai gudana wanda ya wajaba ya zama a raye wanda ake sabuntawa a cikin dukkan lokuta.
Hakanan Allah Ta’ala ya fada a cikin littafinsa mai girma cewa:
Muminai maza da muninai mata kuwa masoyan juna ne: Suna yin umurni da kyakkyawa abu suna kuma hana mummunan, suna kuma tsai da salla suna ba da zakka suna kuma bin Allah da Manzonsa. Waxannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah kuwa Mabuwayi ne Mai hikima. [Tauba: 71]
Ayar tana nuni zuwa ga cewa, muminai maza da muminai mata masoyan junansu ne, don haka
lokaci. Annabi (S.A.W) ya kasance yana yin da’awa a Masallaci, yana yi a kan haya da kasuwa da wuraren da ke tara jama’a. Hakanan ya kasance yana yin mu’amala da kowa, har da wadanda suka cutar dashi suka ki karbar da’awarsa. Wannan ita ake kira da da’awa ta hakika wadda take daukar sakon Musulunci zuwa ko’ina a bayan kasa.
A karshe, ba zai yiwu a cimma kowane irin ci gaba ba a cikin al’ummar Musulmi sai ta hanyar kira zuwa ga addinin Allah Ta’ala. Wajibi ne a kan kowane Musulmi ya dauki wannan babban aiki a kan wuyansa, ya yi kokari wurin yada alheri a cikin al’ummarsa da abin da zai samar da gyara na hakika da samar da al’umma mai tsayuwa a kan kyawawan dabi’u da tsai da adalci.
suna yin aiki a tare don tabbatar da aikin alheri, suna hanuwa ga barin aikata munanan ayyuka, suna kuma tsai da salla suna ba da zakka. Duk wannan yana karkashin kira zuwa ga addinin Allah, ta yadda muminai suke taimakekeniya a tsakaninsu don yada ayyukan alheri ingantattu da tabbatar da adalci a cikin al’umma.
Lalle yin kira zuwa ga addinin Allah yana a matsayin sakon da wajaba ga kowane Musulmi yayi riko dashi, ba tare da duba zuwa ga yanayin da aka tsinci kai a ciki ba. Hakanan kuma ya wajaba a kan Musulmi yayi aiki tukuru wurin kira zuwa ga addinin Allah da isar da abin da yake koya zuwa ga wadanda ba su sani ba. Hakanan ya yi koyi da Manzon Allah (S.A.W) wanda ya yi kira zuwa ga addinin Allah a kowane irin wuri da kuma kowane

362
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya