Kuma kada ku auri wadda iyayenku maza suka aure ta cikin mata, sai fa abin da ya riga ya shuxe. Lalle yin hakan ya kasance alfasha ce kuma abu ne da zai jawo fushin Allah, kuma tafarki ne wanda ya yi muni
An haramta muku auren iyayenku mata da ‘ya’yanku mata da ‘yan’uwanku mata da gwaggonninku da yagwalgwalanku da ‘ya’yan xan’uwa da ‘ya’yan ‘yar’uwa da iyayenku waxanda suka shayar da ku da ‘yan’uwanku mata ta wajen shayarwa, da iyayen matanku da agololinku waxanda suke cikin gidajenku, waxanda matan da kuka tava saduwa da su suka haife su, in kuwa ba ku tava saduwa da su ba, to babu laifi a kanku, da matan ‘ya’yanku maza waxanda suke na tsatsonku; haramun ne kuma ku haxa ‘yan’uwa mata biyu, sai dai abin da ya wuce a baya[2]. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai jin qai
Katika masu alaka
Nuna katika