Tsare Amana Tsare Rayuwa Ne
See other videos from same category
Ya ku waxanda suka yi imani, duk wanda ya yi ridda daga cikinku, ya bar addininsa, to (ya sani) Allah zai kawo waxansu mutane da Yake son su suna son Sa, suna masu qasqantar da kai ga muminai, suna masu nuna wa kafirai isa, suna yin jihadi don xaukaka kalmar Allah, kuma ba sa jin tsoron zargin wani mai zargi. Wannan falalar Allah ce da Yake bayar d...
Ku Za Mo Cikin Masu Gaskiya A Kowane Yanayi
Akwai wasu mazaje daga muminai da suka cika abin da suka yi wa Allah alqawari da shi; akwai daga cikinsu wanda ya haxu da ajalinsa, akwai kuma daga cikinsu wanda yake sauraron (ajalin); kuma ba su yi kowace irin savawa ba (game da alqawarin)Don Allah Ya saka wa masu gaskiya a kan gaskiyarsu, Ya kuma azabtar da munafukai idan Ya ga dama, ko kuma Ya...
alle masu taqawa suna cikin inuwoyi da idanuwan ruwaDa kuma ababan marmari daga abin da suke sha’awaKu ci kuma ku sha kuna masu farin ciki saboda abin da kuka kasance kuna aikatawaLalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
Da yawa daga cikin ma’abota littafi sun yi burin ina ma a ce su mayar da ku kafirai bayan imaninku, saboda hassada daga zukatansu, bayan kuma gaskiya ta bayyana a gare su. Don haka ku yi afuwa ku kawar da kai har sai Allah Ya zo da al’amarinsa. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai
Kuma sakamakon mummunan (abu) shi ne mayar da mummuna kamarsa; to wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata, to ladansa yana wurin Allah. Lalle Shi ba Ya son azzalumai