Nana Maryam a yanayin raxaxi!

Nana Maryam a yanayin raxaxi!

Yayin da muke karanta labaran manyan mutane, za mu iya ganin qarfin su amma kuma mun manta irin yanayin da suka keto ta cikinsa na tsoro da raxaxi. Don haka Alqur’ani yana xaukar mu zuwa ga xaya daga cikin mafi tsananin yanayi da ya auku a rayuwar Nana Maryam; wato lokacin da za ta haihu, ga ta ita kaxai ce, kuma ta yi nisa daga danginta, tana cike da tsoron raxaxin abin da ke cikin ta da kuma tsoron yadda za ta fuskanci mutane da wannan yaron bayan ta haife shi.
Allah Ta’ala yace: “Sai ciwon naquda ya tilasta mata zuwa ga kututturen dabino, ta ce: “Ina ma na mutu tun kafin wannan (abu ya faru), na kuma kasance yasasshiya, mantacciya!” [Maryam: 23] wato wasu irin kalmomi ne da suke bayyana irin girman abin da take ji na firgici da tsoro. Sai ga kira ya zo mata da busharar samun nutsuwa cewa; “Kada ki yi baqin ciki, haqiqa Ubangijinki Ya sanya qorama a qarqashinki. “Ki kuma girgiza kututturen dabinon nan zai zubo miki da lubiyar dabino nunanniya. “Don haka ki ci, ki sha, kuma ki kwantar da hankalinki;” [Mayam: 24-26]
Kada ki yi baqin ciki. Ki ci kuma ki sha ki kuma samu nutsuwa. Ga su dai kalmomi ne masu sauqi, amma kuma sun zo a daidai lokacin da ya kasance jin raxaxi ya fi magana girma. Kuma za ta iya kasancewa saboda wannan ne ma qissar Nana Maryam ta zamana ta fi zamowa kusa da zuciya, saboda ba ta hakaito mu’ujiza ba ce ba kawai, a’a tana hakaito labarin wata mata da ta shiga yanayin tsoro da raxaxi, sai kuma ta samu rahamar Allah a tattare da ita a yanayi da ya zamo mafi tsananin yanayi a tattare da ita.

9
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Yi tarayya