Me Ya Sa Alƙur’ani Ke Magana Game da Kanka?
Duniya tana bibiyar ‘yan wasa, ta fuskar; sauri da qarfi da kuma gogewa.
Sai dai shi kuma Alqur’ani yana maido da gani zuwa ga wani abu na daban, wato mutum ya dawo da dubansa zuwa ga kansa.
Yana kiransa da ya dawo zuwa ga waxannan tambayoyi da ba sa bayyana a fuskar talabijin, wato me ya sa muke shiga cikin damuwa?
Me ya sa a ko da yaushe muke binciken neman ma’anar wani abu? Kuma me ya sa wasu mutane suke jin ba su da aikin komai a kansu koda kuwa sun rabauta da samun abin da suke nema?
Alqur’ani yana cewa: “Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba? Zariyat: 21
Kai ka ce saqon yana cewa, ka fara tunani game da kanka.
Abubuwan da kake ji a rai da fixirarka, yanayin yadda zuciyarka take yayin da take son abu ko take tsoron wani abu ko yayin da wani abu zai rushe ya ruguje.
Da yawa daga cikin mutane suna sanin Allah ne ba ta hanyar doguwar jayayya ba, sai dai suna sanin shi ne ta hanyar ta’amulli na gaskiya game da kawunan su. A cikin wani salon tsari mai ban mamaki da ke cikin ran xan’adam. Hakanan a cikin wannan zuzzurfar buqatar ta neman samun aminci, za ta iya yiwuwa mafi kusancin hanyar da za ta kai ga sanin haqiqanin lamari ba ta yi nesa da kai ba kamar yadda kake zato ba.
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category