Alkawurra da Gargadi
See other videos from same category
Mala’iku da Jibrilu suna ta saukowa da dukkanin al’amura a cikinsa da izinin Ubangijinsu Aminci ne shi (daren dukkansa) har zuwa hudowar alfijir
Yana shirya al’amari daga sama zuwa qasa sannan (al’amarin) ya hau zuwa gare Shi a cikin wani yini da gwargwadon (tsawonsa) yake shekara dubu ne daga abin da kuke qirgawa Wannan (Shi ne) Masanin voye da sarari, Mabuwayi, Mai rahama
Kyakkyawan Fatan da Kuma Tsoro
Kuma al’amarinmu bai zamanto ba face kalma xaya kamar qiftawar idoHaqiqa kuma Mun hallakar da ire-irenku , to ko akwai mai wa’azantuwa?Kuma kowane abu da suka aikata yana cikin littattafaiKowane qaramin abu da babba kuma suna nan a rubuceLalle masu taqawa suna cikin gidajen Aljanna da qoramu
Wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qaga wa Allah qarya ko kuma ya qaryata gaskiya lokacin da ta zo masa? Yanzu ashe babu mazaunar kafirai a cikin Jahannama? Waxanda kuma suka yi jihadi saboda Mu to tabbas za Mu shiryar da su hanyoyinmu , kuma lalle Allah Yana tare da masu kyautatawa
Lalle Allah Ya sayi rayuka da dukiyoyin muminai daga wurinsu cewa suna da Aljanna: Za su yi yaqi saboda Allah, sai su kashe su ma kuma a kashe su. Alqawari ne na gaskiya da Ya xaukar wa kansa a cikin Attaura da Linjila da Alqur’ani. Wane ne ya fi Allah cika alqawarinsa? Saboda haka sai ku yi farin ciki da cinikin nan naku da kuka yi da Shi. Wannan...