Me Yasa Muke Rayuwa? Mece ce Manufar Samar Damu?
Ka xan yi tunani na xan lokaci, ka xan dakata daga yin aiki, ka qaurace wa hayaniya da labaran da suke da alaqa da ita, ka zauna kai kaxai tare da wannan tsohuwar tambayar kuma sabuwa, wato:
Saboda me muke rayuwa?
Kuma saboda me a ko da yaushe muke jin muna buqatar samun wani abu ko da kuwa mun mallaki dukkan komai.
Kowane mutum a duk inda ya kasance yana xauke da wannan tambayar a cikin ransa, kai ka ce, wani maxauri ne da yake xauremu gabaxayanmu da wata haqiqa da bamu santa ba.
Alqur’ani ba ya kawo shiryayyiyar amsa da za ta tafiyar da hankali, sai dai yana buxe qofa mai faxi don yin tunani game da ma’anar samuwa.
Allah Ta’ala yana cewa: “(Allah Ya ce da su): “Ko kuna tsammani ne cewa Mun halicce ku ne ba manufa kuma ku ba za a dawo da ku gare Mu ba?” [Muminun: 115)
Tambaya ce mai girgiza ran xan’adam: shin zai yiwu ka zo wannan duniyar ka girma, ka yi aiki ka ji raxaxi, sannan komai ya wuce ba tare da wata manufa ba.
A yayin da kake yin tunani a irin wannan salon, za ka gane ashe rayuwarka ba a haka kawai ta samu ba.
Sannan wannan zuzzurfan abin da kake ji a rai kuma kake neman sanin ma’anarsa ba wahami ba ne, sai dai shi wata manuniya ce.
Manuniya ce da take faxa maka cewa, kai fa ba gangar jiki ba ce da take rayuwa ta mutu ba kawai, a’a kai ruhi ne da yake neman tafakinsa. Kuma a cikinsa yana jin cewa wannan hanyar ba mai qarewa ba ce da qarewar duniya ba.
Manufar ba ita ce a guje wa yanayin da ake ciki ba, ko a maqale wa wasu tsaruka ba, a’a manufar tana cikin gano dalilin samuwarka, da kuma gano cewa akwai mahaliccin da ya sanka, kuma yake kusa da kai sama da yadda kake zato, yake kuma jin tausayinka sama da dukkan wani abu ya faru da kai kake ganin jin qai ne a tattare da kai.
Saboda me muke rayuwa?
Saboda rayuwarka wani saqo ne. Saboda samuwarka ba don wargi ba ne.
Zuciyar da take irin wannan tambaya, to wannan shi ne matakinta na farko zuwa ga cimma haqiqanin gaskiya
النص
Bidiyoyi masu alaka
See other videos from same category