Gidan Lahira Shi ne Gidan Tabbata

Gidan Lahira Shi ne Gidan Tabbata

Muna rayuwa a wasu irin gidaje....sai dai kuma ba gidaje ne na dawwama har abada ba.
Watarana za mu bar su....su dawo babu komai a cikinsu.
Don haka zuciyoyinmu suna neman gidan da ba za mu ji tsoron barinsa ba...
Gida ne da mutuwa ba ta kwankwasa shi ta shiga.
Alkur’ani yana ambaton wannan gidan da; Gidan tabbatuwa
Wannan ba hikaya ba ce...a’a yakini ne.
Allah Ta’ala ya ce:
Ku sani cewa, ita dai rayuwar duniya ba wata aba ba ce sai wasa da sharholiya da qyale-qyale da kuma fariya a tsakaninku da takara wajan nuna yawan dukiya da ‘ya’yaye; ta yi kama da ruwan saman da tsirransa suka bai wa manoma sha’awa, sannan duk ya bushe, sai ka gan shi fatsi-fatsi, sannan kuma ya zama dudduga; a lahira kuwa akwai azaba mai tsanani da gafara daga Allah da kuma yarda. Rayuwar duniya ba komai ba ce sai jin daxi mai ruxi. (Hadid: 20)
Rayuwa ta hakika ba a nan take ba....a’a tana can (lahira).
A nan muna jin radadi....a can kuma muna samun waraka.
A nan muna tozarta...a can kuma muna samun shiriya.
A nan muna rarrabuwa...a can kuma muna samun haduwa
Alkur’ani yana sirranta zance: kowane taki a nan na dan lokaci ne....duk kuma abin da ka zartar a yau, to dashi za a gina maka gobenka ta har abada.
Kofar gidan tabbatuwa a bude take har yanzu...tafiyar kuma tana farawa ne daga gaskata kanka da ka yi.

408
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya