Ladabin Neman Izini

Ladabin Neman Izini

Kofa ba katako ba ne kawai...Kofa tana da ma’ana.
A bayan kowace kofa...akwai wata zuciya da take hutawa ko wasu iyalai da suke haduwa ko wata rai da take neman aminci.
Saboda haka ne ma Alkur’ani ya koyar da wani ladabi mai girma:
“Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini, kuma kun yi sallama ga masu su. Wannan kuwa shi ya fi alheri a gare ku don ku wa’azantu. To idan ba ku sami kowa a cikinsu ba to kada ku shige su har sai an yi muku izini; idan kuwa aka ce da ku ku koma sai ku koma; wannan shi ya fi tsarki a gare ku. Allah kuwa Masanin abin da kuke aikatawa ne. [Nur: 27-28]
Neman izini...girmama kususiyar wani ne
Aminci ne da yake rigayar taku.
Aminci ne da yake rigayar haduwa.
Ba kawai furta kalmar “Shin in shigo” ba... a’a sanarwa ce cewa ina kwankwasa zuciyarka kafin na kwankwasa gidanka.
Ladabi ne karami...amma kuma yana samar da al’umma babba da za ta ginu a kan tsarki da jin kunya.
Wanda bai koyi neman izini ba...ba zai koyi ladabin rayuwa ba

النص

377
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya