Allah ba ya Son Mabarnata

Allah ba ya Son Mabarnata

Barna a bayan kasa shi ne aikata abin da zai sabbaba fasadi, wannan kuma ya hada da dukkan abin da zai bayu zuwa ga rusa tsarin da Allah Ta’ala ya halicci wannan duniyar a kansa. Lallai Allah Ta’ala ya halicci duniya a bisa yanayi ingatacce, ya sanya mata dukkanin wani abu da take bukata don ta zama wuri mai inganci da za a iya rayuwa a cikinsa, hakanan ya yi mata albarka ya sanya ta ta zamo wurin zama da kuma rayuwa. Sai dai dan’adam saboda barnarsa, zai iya bata wannan duniyar, ya juyar da abin da yake mai amfani ya koma zuwa mai cutarwa. Wannan barnar za ta iya zama daga daidaikun mutane ce ko kuma daga al’umma ce ko kuma ta dalilin siyasa ce.
Allah Ta’ala yana fada a cikin littafinsa mai girma:
Kuma ka tuna sa'adda Ubangijinka Ya ce da mala'iku: “Lalle ni zan sanya wani halifa a bayan qasa.” Suka ce: “Yanzu za Ka sanya mata wanda zai yi varna a cikinta kuma ya zubar da jini, alhali ga mu muna tasbihi tare da gode Maka, kuma muna tsarkake Ka?” (Allah) Ya ce: “Ni fa tabbas Na san abin da ku ba ku sani ba.” [Bakara: 30]
wannan ayar tana bayyana irin yadda mala’iku suka nuna jin tsoronsu na barnar mutane a bayan kasa. Sai dai Allah Ta’ala ya san cewa, barnar ba ita ce karshen lamari ba, a’a ita wani yanki ne na hikimarsa game da halittar dan’adam din. Lallai lalacewar duniya bai takaita a kan lalacewar al’umma ba, a’a ya hada har da yanayin tsarin mutum da ayyukansa da suke cutar da al’umma wadanda kuma suke bayuwa zuwa ga samun fitintinu da matsaloli.
Barna a bayan kasa tana iya zuwa ta fuskoki mabambanta, wanda ya hada daga daidaikun laifuka su bayu zuwa ga lalacewar mutum a karan-kansa, sannan zuwa ga lalacewar al’umma wanda ya samu ta hanyar yada fitintinu da shubuhohi. Don haka ta hanyar laifuffuka da barnar daidaikun mutane, mutum zai fara lalata kansa a karan-farko, Allah Ta’ala yana cewa:
Kuma idan ya juya baya, zai yi ta yawo a cikin qasa don ya yi varna a cikinta, kuma ya lalata amfanin gona da dabbobi. Allah kuwa ba ya son varna. [Bakara: 205]
Barnar da mutum zai aikata tana tashi ta shiga wurin da yake rayuwa, ta yadda mutum zai yada munanan dabi’u wadanda za su yi tasiri a kan wadanda suke tare dashi, kamar yadda mabarnata suke kokarin ba wa kansu hanzarin cewa, su fa manufarsu ita ce kawo gyara, yayin da a hakikanin lamari su ne mabarnata, kamar yadda Allah Ta’ala ya ce: Suna yin umurni da kyakkyawa abu suna kuma hana mummunan, suna kuma tsai da salla suna ba da zakka suna kuma bin Allah da Manzonsa. Waxannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah kuwa Mabuwayi ne Mai hikima. [Tauba: 71]

396
Video Translations
Saukewa
  • Hd Version ( Google Drive )

Bidiyoyi masu alaka

See other videos from same category

icon

Yi tarayya